Ma’aikatan majalisar dokokin kasa, karkashin inuwar kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya, sun dakatar da yajin aikin da suke yi a yau Talata.
Ma’aikatan sun fara yajin aikin ne a ranar Litinin, wanda hakan ya gurgunta ayyukan Majalisar na tsawon mako guda.
Shugaban kungiyar PASAN, reshen majalisar kasa, Sunday Sabiyi, wanda ya yi wa ‘yan majalisar jawabi a ranar Talata ya ce, za a dakatar da yajin aikin har sai an sanar da su.
Ya ce, “Shugaban kasarmu ya yi magana kuma mun ji, sun ce zuwa watan Yuli za mu samu amincewa kuma mu kammala aiwatarwa kuma za a biya alawus din a karshen watan Yuni.
“Shugaban majalisar dattawan ya ce bayan an biya alawus-alawus din nan da karshen watan Yuni, zai kira taron zauren gari. Idan bai kira taron majalisar gari ba, za mu sake kiran wani yajin aikin.
“A saboda haka ne muka dakatar da yajin aikin a yanzu. Don haka kowa ya je ya huta, ya yi wanka ya ci gaba da ayyukan yini.”