Ma’aikatan majalisar dokokin jihar Taraba a karkashin kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya (PASAN), sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani kan rashin biyan alawus-alawus da gwamnatin jihar ke yi.
Kungiyar ta PASAN ta fitar da sanarwar yajin aikin ne a ranar Litinin din da ta gabata ta wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta na jiha Ibrahim Bala Yusuf tare da Sakatarenta Abdullahi Abubakar.
Sun bayyana alhininsu cewa, duk da yunƙurin da ƙungiyar ta ƙulla na ganin gwamnati ta yi zaman tattaunawa a kai a kai, gwamnati a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Darius Dickson Ishaku ta ci gaba da yin kunnen uwar shegu da halin da suke ciki.
Sanarwar ta kara da cewa “Bayan cikar wa’adin kwanaki bakwai da aka baiwa shugabannin wannan majalisa kan batutuwan da suka shafi alawus alawus na ma’aikatan wannan majalisar, shugabancin wannan shahararriyar kungiyar ba ta da wani zabi da ya wuce ta jagoranci. membobin wannan kungiya su nisanta kansu daga aiki daga ranar Litinin 7 ga Nuwamba, 2022”.
Ya ce, ba za a bari wani ma’aikaci ya shiga harabar majalisar dokokin jihar ba, inda ya sha alwashin ba zai dakatar da yajin aikin ba har sai an biya musu bukatunsu.
Da aka ayyana yajin aikin, shirin gwamnatin jihar na gabatar da kasafin kudin 2023 a wannan mako ba zai sake fitowa fili ba.


