Gwamnatin tarayya ta jaddada bada tabbacinta na daukar matakan shawo kan matsalar tabarbarewar harkokin lafiya, a Najeriya.
Karamin Ministan Lafiya, Joseph Ekumankama ya yi magana da manema labarai a ranar Litinin a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Ebute Meta, Legas.
Ya kaddamar da Cibiyar Orthopedic da Trauma, Molecular Building Complex, Oxygen gas plant, Clinical Training Centre, da Ultra-Modern Theater.
Ekumankama ya yarda cewa yawan ƙaura na ma’aikatan kiwon lafiya matsala ce kuma abin damuwa ne.
“Babban kalubalen da bangaren ke fuskanta a halin yanzu shi ne likitoci da ma’aikatan jinya da ke barin kasar,” in ji NAN.
Ministan ya roke su da su ci gaba da zama a Najeriya domin ganin kokarin gwamnati.


