Ƙungiyar ma’aikatan jinya da unguzomomi ta kasa, ta fara yajin aikin gargaɗi na mako guda a faɗin ƙasar.
Ƙungiyar mai mambobi aƙalla 25,000 ta ca ta fara yajin aikin ne domin nuna rashin jin daɗinta kan rashin albashi mai kyau da ƙarancin ma’aikata da rashin biyansu alawus da kuma rashin kariya a wajen ayyukansu.
Shugaban ƙungiyar, Morakinyo Rilwan ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa sun yanke shawarar fara yajin aikin ne bayan ƙarewar wa’adin kwanaki 15 da ƙungiyarsu ta bai wa gwamnati.
Yajin aikin dai ya shafi ma’aikatan jinya da ungozomomin da ke aiki a asibitocin gwamnatin tarayya a cewar shugaban ƙungiyar.
Mataƙin ma’aikatan jinyar na zuwa ne yayain da ake ci gaba da takun saƙa tsakanin ƙungiyar likitocin ƙasar da gwamnatin tarayya kan walwalar likitocin.