Ministan lafiya a Najeriya ya ce, ma’aikatan jinya da ungozoma ƙarƙashin ƙungiyar National Association of Nigerian Nurses and Midwives (NANNM) sun janye yajin aikin da suka fara yi.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a yau Juma’a, Ali Pate ya ce sun ɗauki matakin janye yajin ne saboda yarjejeniyar da suka cimmma da gwamnatin tarayya bayan wata ganawa a yau ɗin.
A ranar Talata ne ma’aikatan jinyar suka fara yajin aikin saboda abin da ƙungiyar tasu ta bayyana da “gazawar gwamanti wajen biyan buƙatunsu cikin wa’adin kwana 15 da ta bayar” ranar 14 ga watan Yuli.
Akaasrin buƙatun sun jiɓanci walwalar ma’aikata, da alawus-alawus a asibitocin gwamnatin tarayyar Najeriya.