Mataimakin shugaban jami’ar jihar Osun Uniosun, Farfesa Clement Adebooye, ya roki sabbin ma’aikatan jinya na makarantar da kada su gudu daga kasar.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwa/ Rantsarwa karo na 3 da aka yi wa sabbin ma’aikatan jinya 40 da suka yi rajista a cibiyar, ya roki ma’aikatan jinya da su jajirce su ba da gudummawarsu wajen ci gaban fannin kiwon lafiyar kasar nan.
A yayin da yake jaddada bukatar gwamnati a matakai daban-daban na samar da yanayi mai kyau ga ma’aikatan kiwon lafiya a kasar nan, ya bukaci sabbin wadanda aka horas da su da su kasance cikin tsarin ci gaban kasar nan.
“Tare da ayyukan da kuke yi a wannan sana’a za ku iya zuwa ko’ina a duniya amma zan fi so idan kun tsaya a Najeriya. Na san kuna son barin kasar nan. Najeriya za ta yi kyau.


