Asibitin koyarwa na jami’art jihar legas ya ce, fiye da ma’aikatan jinya 150 ne suka bar aiki a asibitin cikin shekara uku da suka gabata.
Babban Daraktan asibitin Farfesa Adetokunbo Fabamwo ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabi ga taron manema labarai a jihar.
Farfesa Fabamwo ya ce barin aikin ma’aikatan jinyan ya samo asali ne sakamakon ficewa daga Æ™asar domin tafiya Æ™asashen waje da ma’aikatan lafiya a Æ™asar suka gano.
Daraktan asibitin ya ce Æ™oÆ™arin da gwamnatin jihar ke yi na maye guraben ma’aikatan ne ya hana tsayawar aiki a asibitin.
Ya ƙara da cewa a baya-bayan nan adadin takardun masu neman aikin jinya da aikin likita ya ragu a asibitin.