Kungiyoyin ma’aikatan jami’o’in waɗanda ba malamai ba da ake kira da (SSANU da NASU), sun gudanar da wata zanga-zanga saboda riƙe musu kuɗin albashinsu na watanni.
Masu zanga-zangar sun fara ne daga filin taro na Unity Fountain a Abuja.
Ma’aikatan sun zargi gwamnatin ƙasar ta riƙe musu albashinsu na watanni huɗu a lokacin da suka yi yajin aki a 2022, da kuma yarjejeniyar 2010 da suka cimma da gwamnatin wadda har yanzu ba a cika musu ba.