fidelitybank

Ma’aikatan INEC a Kano sun koka a kan kudin aikin su

Date:

Wata matsala da ake fuskanta a jihar Kano, ita ce ta rashin biyan ma’aikatan INEC na wucin gadi kuɗaɗensu na alawus.

Wani da BBC ta zanta da shi ya ce tun daga lokacin da suka fara karɓar horo kan wannan aikin, ba a basu komi ba, kuma sai da suka kwashe kwana biyu suna barci a kan benci.

“Kwana na ɗaya da yini guda ban ci komi ba, babu wanda ya kawo mana ko da ruwan sha balle maganar kuɗin mota, kuɗi muka ara muka zo nan.

“Da muka zo nan an faɗa mana ana bayar da alawus na dubu huɗu amma a yanzu cikin ƙasa da awa guda an ce wai an koma bayar da 3,500, an rage ɗari biyar,” in ji wani ma’aikaci da BBC ta zanta da shi.

Karanta Wannan: Da Dumi-Dumi: An kona ofishin INEC na Takai a Kano

Duk da cewa sunayensu na cikin jerin waɗanda za su yi zaɓen gwamna, amma ya ce shi ba zai yi wannan aiki ba a lokacin zaɓen gwamna mai zuwa.

Sai dai, mun tuntuɓi jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar INEC Zainab Aminu Abubakar domin ji daga gareta, inda ta ce bata da matsaniyar wannan magana, amma ta ce za su yi bincike kan lamarin.

breaking news in nigeria today punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp