A kowacce ranar 1 ga watan Mayu ake yin bikin ranar Ma’aikata ta Duniya
Wannan rana na da dumbin tarihi a cikin rayuwar ‘yan kwadago a kasashe daban-daban.
Ƙungiyoyin kwadago a kasashen duniya kan gudanar da manya -manya taruka kuma su fito su bayyana ire-iren abubuwan da ke ci masu tuwo a ƙwarya game da lamarin rayuwar ma’aikata.
A babban birnin tarayya, ma’aikata sun yi gangami a dandalin Eagle Square.