Hukumar Ƙwadago ta Kasa ta ce, ma’aikata na cikin wani hali, kuma babu wani sauyin a zo a gani da aka samu tun bayan kama mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
A wata tattaunawa da BBC, albarkacin ranar ƙwadago ta duniya, sakataren ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, Kwamared Nasir Kabir ya ce ci gaba kaɗan ne kawai za a iya cewa ma’aikata sun samu a ƙarƙashin gwamnati mai ci.
Ya ce “abin farin ciki ne sake zagayowar ranar ma’aikata ta duniya, amma maganar gaskiya al’amuran da ma’aikata (a Najeriya) suke ciki da abubuwan da suke fama da su ba abin murna ko farin ciki ba ne.”
Abubuwan da ya bayyana cewa su ne manyan ƙalubalen da ma’aikata a Najeriya ke fuskanta su ne.
A cewar kwamared Nasir ƙarancin albashin ma’aikata a Najeriya ba zai ishi magidanci ya sayi buhun shinkafa da zai ciyar da iyalansa ba.
A cewarsa “idan ka duba a halin yanzu ma’aikaci a Najeriya na cikin hali ne na lahaula.”
A lokacin da aka tambaye shi ko ma’aikata sun samu ci gaba ƙarƙashin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, sai ya ce “ban da ci baya, babu abin da ma’aikata suka gani.”