Ma’ikata fararen hula da ke aiki a cibiyoyin ma’aikatun tsaron sojoji a kasar nan, sun gudanar da wata zanga-zanga tare da rufe ma’aikatar tsaron sojoji da ke Abuja.
Ma’aikatan dai sun gudanar da wannan zanga-zangar ne bisa zargin da suke cewa sojoji na cin zarafin su, inda da dama daga cikin su ke ci gaba da zama a tsare a hannun sojoji.
Sun bayyana cewa, jami’an sojoji na ƙuntata musu ta hanyar dukan su da kuma kulle su a gadirum, duk da cewa su fararen hula ne ba sojoji ba.
Masu zanga-zangar sun kuma bayar da misali da wani mai suna Ambrose Akhigbe, wanda mataimakin darakta ne a makarantar sakandiren ‘ya’yan sojoji da ke jihar Legas da wani jami’in soji ya azabtar da shi a ranar Litinin ba tare da la’akari da dokokin da suka shafi ma’aikatan gwamnati fararen hula ba.
Bayan aukuwar wannan zanga-zanga ta wadannan ma’aikatan, Dakta Ibrahim Abubakar Kana babban sakatare a ma’aikatar tsaro ta kasa ya yi wa ma’akatan jawabi, cewa za a duba korafi na su.
Ya kuma ce an kama dukan wadanda ake zargi da hannu a cin zarafin ma’aikata fararen hulha da ke cibiyoyin tsaron.
An dade ana bayyana cewa jami’na sojoji na yi wa ma’aikta fararen hular gwale-gwale tare irin na sojojin, a duk lokacin da wani abu ya faru tsakaninsu, sai dai wannan shi ne kusan karo na farko da aka samu sun fito sun bayyana damuwarsu a fili.