Daraktan yada labarai na zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya bayar da gargadi ga wadanda ke bayyana Tinubu a matsayin dillalin miyagun kwayoyi.
Onanuga ya yi gargadin cewa kwanakin masu yin amfani da wasu maudu’i wajen caccakar Tinubu ya cika.
Ya ce, wadanda ke da hannu a wannan maudu’in za su fuskanci fushin Allah a kan mugayen sakonnin da ake yi wa Tinubu.
Kafin zaben shugaban kasa, an zargi Tinubu da kasancewa dillalin miyagun kwayoyi lokacin da yake kasar Amurka.
Wasu ‘yan Najeriya sun yi kira da a kama shi tare da dakatar da shiga yakin neman zaben shugaban kasa.
Bayan nasarar da ya samu, wasu ‘yan Najeriya sun yi ta kiraye-kirayen a kama shi a daure shi.
Da yake mayar da martani, Onanuga ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “Duk wadancan da suka wallafa mai suna #TinubuTheDrugDealer#TinubuFor Prison, kwanakinku sun cika.
“Wata rana, za ku fuskanci fushin doka da kuma Allah, saboda yada karyar karya a kan zababben shugaban Najeriya.”