Gwamnatin jihar Zamfara, ta koka kan yadda jama’a ke sare bishiyoyi domin samun gawayi ta hanyar ƙona itacen.
Gwamantin dai ta ce hakan na barazana ga shirin da take yi na magance kwararowar hamada da zaizayar ƙasa a faɗin jihar.
Kassim Sani Shantalin Kaura, shi ne kwamishinan muhalli da ma’adanai da albarkatun ƙasa a jihar Zamfara, ya bayyana wa BBC cewa hakan na matuƙar illa ga muhalli.