Ƙasar Lithuania ta sanar da daina sayen iskar gas daga Rasha, Estonia wadda maƙociyarta ce a yankin Baltic ta sanar da ɗaukar irin wannan matakin.
Gwamnatin ƙasar ta ce, tana da zimmar daina amfani da gas ɗin Rasha nan da farkon “lokacin zafi” na wannan shekara.
Ministocin Estonia sun ce sun cimma yarjejeniya da Finland don ba ta damar shiga da gas ɗin girki.
“A yau mun ɗauki matakin daina sayen gas ɗin Rasha. Ba zai yiwu mu ci gaba da tallafa wa Rasha ci gaba da yaƙi ba,” a cewar Firaministan Estonia Kaja Kallas.
Duk da cewa kashi 7 cikin 100 na makamashin Estonia ne kawai gas, kusan dukkansa na fitowa ne daga Rasha. In ji BBC.