Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Romelu Lukaku, ya tabbatar a ranar Asabar cewa, zai koma kungiyar AS Roma a wannan kakar cinikin.
Lukaku ya yi magana da kafar yada labaran Belgium Het Laatste Nieuws a gefen gasar matasa a Boom, lardin Antwerp, inda dansa ya fara fitowa a Anderlecht.
Tsohon dan wasan Manchester United da Everton ya ce zai tafi Rome ranar Lahadi domin rattaba hannu kan kwantiragi da AS Roma.
“Ina cikin damuwa… Gobe zan tashi zuwa Rome don sanya hannu,” in ji Lukaku.
Kalaman Lukaku sun zo ne yayin da Chelsea, kulob dinsa na yanzu, da kuma wakilan Giallorossi ke Landan suna murza cikakkun bayanai kan yarjejeniyar.
Dan kasar Belgium ya shafe kakar wasan da ta gabata a matsayin aro a Inter Milan.
Ba ya cikin shirin kocin Chelsea Mauricio Pochettino na wannan kakar.


