Luis Diaz ya kammala komawa Bayern Munich daga Liverpool kan fam miliyan 65.5.
Ɗan ƙwallon tawagar Colombia ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka huɗu da ƙungiyar Jamus, hakan ya kawo karshen shekara uku da rabi da ya yi a Liverpool.
Mai shekara 28 ya bar sansanin Liverpool a nahiyar Asia lokacin da za ta kara da AC Milan ranar Asabar, saboda jita-jitar da ta yi yawa kan makomar ɗan wasan a Anfield.
Tun farko Liverpool ba ta amince da tayin fam miliyan 58.6 da Bayern ta fara yi ba, hakan ya sa aka kara kuɗin sayen Diaz daga baya ƙungiyar Anfield ta amince ta kuma yadda yaje Jamus aka auna koshin lafiyarsa.
Diaz ya koma Liverpool daga Porto kan fam miliyan 37 a Janairun 2022, ya ci ƙwallo 41 a wasa 148 a ƙungiyar Anfield.
Ya lashe FA Cup da League Cup a kakarsa ta farko a Liverpool, yana cikin ƴan wasan da suka yi rashin nasara a hannun Real Madrid a Champions League a 2022.
Diaz ya taka rawar gani a kakar da ta wuce a babbar gasar tamaula ta Ingila, wanda ya ci ƙwallo 17 da ɗaukar kofin Premier League.
Tafiyar da Diaz ya yi, Liverpool ta sayar da ƴan wasa kan fam miliyan 115 a bana.
Ta kuma sayi ƴanwasa kan fam miliyan 270 da ya haɗa da Florian Wirtz da Hugo Ekitike da Jeremie Frimpong da kuma Milos Kerkez.
Har yanzu Liverpool na son yin zawarcin ɗan ƙwallon Newcastle, Alexander Isak, wanda bai bi ƙungiyarsa wasannin atisaye da take yi a nahiyar Asia ba.