Kyaftin din Colombia, James Rodríguez, ya dage cewa dan kasarsa Luis Díaz ya yi zabin da ya dace ya bar Liverpool zuwa Bayern Munich.
Ku tuna cewa kwanan nan Diaz ya bar Reds ya koma Bayern Munich a matsayin dindindin.
Dan wasan mai shekaru 28 ya fara buga wa zakarun na Bundesliga wasan sada zumuncin da suka doke Lyon da ci 2-1 a ranar Asabar.
Da yake magana kan komawar Díaz zuwa Bayern, Rodríguez, wanda kuma ya taba bugawa kungiyar ta Jamus a baya, ya ce dan wasan zai taimakawa kungiyar ta Vincent Kompany a wannan sabuwar kakar.
“Ina ganin Luis Díaz ya yi zabi mai kyau. Bayern ta sanya hannu kan babban dan wasa,” in ji Rodríguez ta hanyar The TouchlineX.
“Lucho ya dace da su, Bayern babbar kungiya ce, ina ganin zai taimaka musu sosai.”
Díaz zai yi fatan zai jagoranci Bayern zuwa nasara idan za su kara da Tottenham Hotspur a wasan sada zumunci a ranar Alhamis.