Kotun sauraren kararrakin zaben jihar Abia da ke zama a Umuahia, ta yi watsi da wasu dalilai uku na dan takarar jam’iyyar PDP, Okey Ahaiwe ya gabatar a kan Gwamna Alex Otti.
Kotun da ta yanke hukuncin da misalin karfe 1:20 na rana, ta yi watsi da karar Ahaiwe saboda rashin cancanta.
Ahaiwe ya kalubalanci ayyana Otti a matsayin zababben gwamnan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi.
A cikin addu’ar da ya yi ta bakin Lauyansa, Paul Ananaba, SAN, Ahaiwe ya bukaci kotun da ta tsige Otti tare da bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Dan takarar na PDP ya ce nasarar zaben Otti bai dace da sashe na 77 na dokar zabe ba.
Koyaya, kotun ta yi watsi da duk buƙatun, saboda rashin cancanta.
Nasarar ta jefa dubban magoya bayan jam’iyyar LP da suka fito daga sassa daban-daban na jihar cikin farin ciki ba tare da bata lokaci ba, yayin da suke raye-raye cikin murna da murna a wajen harabar babbar kotun tarayya.
A halin yanzu dai kotun tana gudanar da shari’ar da Ikechi Emenike na jam’iyyar APC ya kai Otti.
Emenike yana rokon kotun da ta tsige gwamna Otti, bisa zargin cewa bai yi murabus daga jam’iyyar APC ba kafin ya koma jam’iyyar LP.
Shi ma dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamna na ranar 18 ga Maris yana ikirarin cewa sunan Otti ba ya cikin rajistar jam’iyyar LP lokacin da ya tsaya takara.