fidelitybank

Lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su fara gani a ƙasa

Date:

Ministan kula da dabbobi na Najeriya, Alhajij Idi Mukhtar Maiha, ya ce ya kamata ƴan Najeriya su fara gajiya da maganar cewa ƙasar na da damarmaki, inda a cewarsa, lokaci ya yi za ya kamata su fara a gani a ƙasa.

Maiha ya bayyana haka a taron tattaunawa wanda jaridar Daily Trust ta shirya na bana, wanda shi ne karo na 22, inda ya ce ya kamata tsare-tsaren harkokin noma su kawo hanyoyin da za a kawo sauyi kan yadda manoma suke noma kawai domin su ci, sai kaɗan suke sayarwa.

Ya ce akwai buƙatar a canja yadda ake kallon harkokin noma da kiwo a ƙasar, sannan ya ƙara da cewa ma’aikatarsa za ta inganta harkokin kiwo.

Sai dai ya ce matsalar rashin tsaro ta shafi harkokin samar da abinci a ƙasar, sannan ya yi kira da rumgumi harkokin noma a damuna da rani, wanda a cewarsa hakan ne kawai zai magance ƙarancin abincin, sannan ya rage farashinsa.

A ƙarshe ya yi kira da a magance matsalar rikice-rikicen manoma da makiyaya, inda ya ce ma’aikatansa na aiki tuƙuru domin magance matsalar.

Tun da farko, shugaban kamfanin Media Trust, Malam Kabiru Yusuf ya ce alƙaluma suna nuna cewa akwai damuwa a ɓangaren samar da abinci a ƙasar.

A jawabinsa a wurin taron mai taken: Samar da abinci: Samar da shi da farashi, ya ce “me ya sa ƴan Najeriya suke shan wahalar samun isasshen abinci? dole mu duba batun nan, muna jira mu ji me masana za su ce game da samar da abincin da farashinsa.”

tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Neja zai haɗa kai da matatar Ɗangote wajen haƙo ɗanyen man fetur

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya nemi aikin haɗin...

Tchiani ya zargi Najeriya, Faransa, China da Amurka wajen cutar da Nijar

Shugaban sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya zargi Najeriya...

An ceto yara 12 da aka yi safararsu a jihar Abia

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce jami'anta sun samu...

A na neman kusan Mutane 400 da suka ɓace a ambaliyar Neja

A na ci gaba da ayyukan ceto bayan ambaliyar...

Mun bayar da hutu ranar Litinin bisa jimamin mutuwar ƴan Wasa – Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar...

Tun farko na shaida wa Tinubu ba zan zaɓe shi ba – Amaechi

Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce...

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka ƴan Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...
X whatsapp