fidelitybank

Lokaci ya yi da za mu hukunta ‘yan siyasa masu ci da addini – EL-Rufa’i

Date:

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya ce, lokaci ya yi da za a cire batun addini daga siyasar ƙasa tare da hukunta ‘yan siyasar da ke amfani da addini a matsayin makamin yaƙin neman zaɓe.

Rahotonni sun ambato gwaman na wannan maganar ranar Talata a lokacin bikin ƙaddamar da babban ofishin ‘gidauniyar zaman lafiya da ci gaba’ ta mai alfarma sarkin musulmi

El-Rufai ya yi kira ga Sarakunan gargajiya da malaman addini da su riƙa gudanar da addu’o’in samun ingantaccen zaɓe da samun zaman lafiya a fadin ƙasar.

Ya ce “Ina so na yi amfani da wannan damar na yi kira ga shugabanninmu da ke nan, masu girma sarakunan gargajiya da malamanmu da su ci gaba da yi wa ƙasarmu addu’o’in samun zaman lafiya da samun ingantaccen zaɓe, tare da yin addu’ar Allah ya zaɓa wa ƙasarmu shugabannin na-gari da za su haɗa kan ƙasar tare da ciyar da ita gaba”

”A matsayina na ɗan ƙasa, kuma gwamna sannan kuma musulmi bana jin daɗin yadda wasu ‘yan siyasa ke amfani da addini da ƙabilanci a matsayin makaminsu na yaƙin neman zaɓe”, in ji El-Rufai.

Haka kuma gwamnan ya ce lokaci ya yi da za a cire batun addini daga siyasar ƙasar tare da hukunta waɗanda ke ƙoƙarin amfani da addinin a matsayin makamin yaƙin neman zabe.

thisday nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp