Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce, yanzu lokaci ya yi da za a sake gina amanar jama’a a harkokin mulki.
Gwamna Uba Sani, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin din da ta gabata, ya bayyana cewa manyan mutane irin su marigayi Cif Moshood Abiola sun yi sadaukarwa sosai domin tabbatar da cewa dimokuradiyya ta samu ci gaba a Najeriya.
Ya ce iyayenmu da suka kafa mu, shugabannin kwadago, kungiyoyin farar hula da masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya sun ba da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban dimokuradiyyar mu, kuma muna bin su bashin godiya bisa irin kokarin da suke yi na soyayya.
“Shekarun da suka gabata na ayyukanmu na dimokuradiyya suna cike da kalubale. Amincewar mutanenmu ga dimokuradiyya da gwamnati sun ragu sosai saboda rikicin tattalin arziki, zamantakewa da siyasa, tare da mummunan sakamako. Yawancin mutanenmu suna jin cewa kasar da shugabanninta ba su damu da su ba.
“Matasan suna ganin kasar nan ba ta damu da makomarsu ba kuma yawancin sassan kasar sun yi imanin cewa ba a ba su hankalinsu ba.
Ya kara da cewa “Wadannan ra’ayi da damuwa suna barazana ga makomar tattalin arzikin kasarmu da kuma burinmu na hadin kan kasa.”
Ya ce yadda ake tsara manufofi da aiwatar da su a Najeriya ba tare da cikakken tuntuba da bin diddigi ba ya sa jama’a su raba kawunansu.
“Saboda haka, kalubalen da ke gabanmu shi ne yadda za mu maido da amanar jama’a ga gwamnati da kuma zaburar da su yadda ya kamata domin gudanar da muhimmin aiki na sabunta kasa, dole ne kasarmu ta koma wani sabon salo.
“Dole ne mu samar da matakai don tabbatar da hada kai, mai da hankali, daidaito da kuma gaskiya wajen tsara manufofi da bayar da hidima.”
“Saukar da madafun iko ita ce hanyar da za a bi, dole ne a ba wa jihohi karin iko don kula da bukatun jama’a tun daga tushe.
“Rarraba madafun iko zai fitar da damar da ake da ita a ko’ina a Najeriya. A jihar Kaduna muna yin kokari da gangan don yada ci gaba ta hanyar mayar da hankali kan yankunan karkara.
“Mun kuduri aniyar sake farfado da tattalin arzikin yankunan karkara ta hanyar bunkasa ababen more rayuwa. Lokacin da muka sa tushen ya zama abin sha’awa ga jama’armu, za a duba ƙaura zuwa birane, jama’armu za su rungumi dimokraɗiyya gabaɗaya a matsayin tsarin da ya dace da jin daɗin rayuwar su da kuma ba su damar gane cikakken ƙarfinsu.