Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo, ya ce, ɓarnar da aka yi wa Afirka lokacin cinikin bayi shekaru da dama da suka wuce sun cancanci a biya su diyya kawo yanzu.
A rubutun da ya yi a shafin sa na tuwita, ya maimaita jawabin da ya yi a wani taro kan batun wariyar launin fata da ake nuna wa yan Afrika. A cewar BBC.
” Lokaci ya yi da yan Afrika maza da mata su miliyan ashirin da suka samu yanci su samu diyyar bautar da su da aka yi.” In ji Akufo-Addo.
Shugaban ya ce, cinikin bayin ne ya janyo matsalar tabarbarewar tattalin arziki a nahiyar Afrika.
Itama Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cinikin bayin a matsayin wani cin zarafi da ya haifar da gudun hijira da ba a taba ganin irinsa ba a duniya.
KARANTA WANNAN: Munafurci Afrika take yi na ƙin goyon bayan Ukraine a farmaki Rasha – Macron
Shugaban Ghanar ya kara da cewa, batun biyan diyyar kan zamo abun muhawara ne idan anzo kan Afirka da ƴan Afirka.
Ya kuma bada misali da cewa, yahudawa da suka tsira a yakin duniya na biyu an basu diyya.
Ya buƙaci ƙungiyar Afirka da ta hada baki da ƙasashen waje domin kwato wa Afrikawan hakkinsu daga kasashen Turai da suka bautar da su


