Jam’iyyar PDP a Legas ta ce mazauna garin na cikin tsaka mai wuya.
‘Yan adawan sun bukaci su zabi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2023.
Jam’iyyar PDP ta yi wannan kiran ne a lokacin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP (PCC), reshen Legas.
Mataimakin mai ba da shawara kan harkokin shari’a, Mustapha Okandeji ne ya rantsar da tawagar mutane 103 karkashin jagorancin Deji Doherty.
Okandeji ya bukace su da su kasance masu bin tsarin mulkin PDP, dokokin zabe, da kuma hada kuri’u ga dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar.
Doherty ya ce lokaci ya yi da jam’iyyar za ta dawo kan karagar mulki a matakin tarayya domin amfanin Najeriya da al’ummar kasar.
Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Legas ya bayyana Atiku da abokin takararsa, Ifeanyi Okowa, a matsayin gogaggun ‘yan takara, masu basira da koshin lafiya.
“Suna gaban duk wanda sauran jam’iyyu za su nuna masa kuma za su fara aiki nan take.
“Muna yin kira ga jama’ar Legas da cewa lokaci ya yi da za su kwato kansu daga kangi.
“Lokaci ya yi da za a ce “ya isa” ga APC,” NAN ta ruwaito yana cewa.


