Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce, harbe-harben da aka samu a kasar a baya-bayan nan inda aka kashe yara goma sha tara da malamai biyu, shi ne ma dalilin da zai karfafa mallakar makamai ba wai haramta yin hakan ba.
Da yake jawabi a wajen taron kamfanonin samar da bindiga a birnin Houston, ya yi watsi da samar da dokokin takaita mallakar bindiga, kuma ya ce, lokaci ya yi da ya kamata a baiwa wasu malamai damar daukar makamai zuwa cikin azuzuwa.
Ya kuma zargi Shugaba Joe Biden da yunkurin amfani da abun da ya faru, don cimma wata manufarsa ta siyasa. In ji BBC.