Hukumar da ke kula da gasar kwallon kafa ta Nigeria Professional Football League, League Management Company (LMC), ta baiwa kungiyar Kano Pillars F.C bukatar komawa filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, biyo bayan umarnin da Ministan wasanni ya bayar na haramtawa kungiyoyin NPFL amfani da filin wasa na MKO Abiola. .
Idan za a iya tunawa dai, kungiyar Kano Pillars ta kwashe sama da wata guda tana gudanar da wasanninta na gida a filin wasa a wani mataki na ladabtar da kungiyar, sakamakon tashin hankalin da ya barke tsakanin jama’a da suka yi kaca-kaca da kungiyar Katsina United a ranar 30 ga watan jiya.
Amma Ministan Wasanni da Ci gaban Matasa, Hon. Sunday Dare, ya bayar da umarnin hana NPFL gudanar da wasanni a filin wasa na MKO Abiola a ranar Litinin din da ta gabata, sakamakon korafin da babban kocin Super Eagles, Jose Peseiro ya yi game da rashin kyawun filin wasa.
Umarnin na ministan ya bayyana cewa, daga yanzu za a yi amfani da filin wasan ne kawai don wasannin da suka shafi kungiyoyin kasa.
A cikin wata wasika da ta aikewa shugaban kungiyar Kano Pillars a ranar Litinin 10 ga watan Yuni, 2022 da LEADERSHIP Weekend ta gani, ta ba kungiyar izinin komawa gidanta tare da buga wasanni a bayan gida, kuma cikin tsauraran matakan tsaro.
Mun kuma amince da wasiƙar Tabbacin Tsaro daga rundunar ‘yan sandan Nijeriya, rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ba da tabbacin tsaro kafin wasa, da lokacin da kuma bayan wasanni.
Za a yi amfani da wasan ranar 33 na Kano Pillars da Wiki Tourists a matsayin gwaji, don sanin ingancin shirye-shiryen su..