Liverpool a shirye take ta sayar da matasan yan wasan ta uku su a wannan bazarar domin sayen Isak.
A cewar jaridar UK Mirror, su ne Luca Stephenson, James McConnell da Lewis Koumas, su ne yan wasa uku da Liverpool za ta sayar.
Reds sun kasance kungiyoyi da suka kashe kusan fam miliyan 300 akan sayen Hugo Ekitike, Florian Wirtz, Milos Kerkez da Jeremie Frimpong.
Trent Alexander-Arnold shi ma ya koma Real Madrid kan fan miliyan 10, yayin da Bayern Munich ta biya kusan fam miliyan 63.5 kan Luis Diaz.
Zakarun gasar firimiya na kokarin siyan dan wasan gaban Newcastle United, Alexander Isak, wanda zai kai fam miliyan 150.
Sai dai Liverpool ta shirya tsaf don barin wasu ‘yan wasa su bar kungiyar, inda Arne Slot ke neman yin garambawul ga ‘yan wasansa.
Stephenson yana da sha’awar Dundee United, Swansea, Reading, Rotherham da kuma Cardiff kan batun aro.
McConnell yana jan hankalin West Brom, Ipswich, Derby, Oxford, Swansea da Metz ta Faransa, yayin da Koumas zai iya tafiya kamar yadda Norwich, Sheffield United, Hull, Preston, Birmingham da Wrexham duk suke sa ido kan halin da yake ciki.