Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bournemouth, ta samu nasarar fita daga ukun ƙarshe a kan Teburin Premier bayan da ta doke Liverpool da ci 1-0, nasarar kuma da ta hana Liverpool ɗin shiga sahun huɗun farko a kan teburin.
Liverpool ta yi rashin nasararsa ne bayan da ta doke Manchester United da ci 7-0 a makon da ya gabata, yayin da ita kuma Bournemouth ta fara wasan a cikin ukun ƙarshe a teburin Premier.
Rashin tsare gida da kyau ne ya sa Philip Billing ya zura ƙwallo a ragar Liverpool daga tazarar yadi takwas.
Karanta Wannan: Flying Eagles ta zama ta uku bayan ta lallasa Tunusia
Liverpool ta samu bugun Fenareti a wasan bayan da ƙwallon da Diogo Jota ya sanya wa kai ta taɓa hannun Adam Smith.
To sai dai Mo Salah – wanda ya zama ɗan wasan da ya fi ci wa Liverpool ƙwallo a gasar Premier inda ya ci ƙwallo ta 129 a makon da ya gabata – ya ɓarar da bugun fenaretin bayan da ya buga ta waje.