Rahotanni sun bayyana cewa, Liverpool ta bayyana dan wasan Juventus Federico Chiesa a matsayin wanda zai maye gurbin Mohamed Salah.
Ana alakanta Salah da komawa kungiyar Al-Ittihad ta kasar Saudiyya a bana a yayin da kungiyar ta Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da kashe kudade.
A cewar Di Marzio, Chiesa ya dawo kan radar Liverpool, bayan gano babban sha’awar Salah daga Al-Ittihad.
Ana kallon Chiesa a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan na Masar a Anfield.
Dan wasan mai shekaru 25 ya nuna shakku kan makomarsa a Juventus a farkon wannan shekarar kuma ya nuna cewa baya tunani sosai kan makomarsa.
Lokacin da aka tambaye shi ko ya sadaukar da Juve, Chiesa ya yi iƙirarin cewa ya mai da hankali ne kawai kan hutun sa.
“Na yi farin ciki da yadda na gama, shekara ce mai matukar wahala a gare ni. Yanzu ina tunanin hutu ne kawai, “in ji Chiesa ga Sky Italia.


