Liverpool ta lashe gasar kofin Carabao bayan ta doke Chelsea da ci daya mai ban haushi.
Wasan an buga shi ne a filin wasa na Wambledon wanda aka kai ruwa aka kai gauro a wasan.
Wasan dai ƴar manuniya ce wadda Liverpool ta lashe irinsa a shekarar bara a hannun Chelsea a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Wasan dai na yau an ƙarƙare shi bayan da Virgyl Van Dyk ya tura ƙwallo da ka a minti sama da 100.