Fitaccen dan wasan barkwanci na Najeriya, Bright Okpocha, wanda aka fi sani da Basketmouth, ya shigar da dansa, Jason Okpocha, a makarantar horar da kwallon kafa ta Liverpool da ke Ingila.
Baban mai alfahari ya raba bidiyon dansa ya isa makarantar ta shafinsa na Instagram ranar Litinin.
Ya yi taken bidiyon; “Tafi kayi daddy abin alfahari. @liverpoolfccamps.”
Abokan aikinsa da magoya bayansa sun yi dandazo a sashen sharhi don taya jarumin barkwanci da dansa murna.
Jason shi ne ɗan Basketmouth tilo tare da matarsa Elsie Uzoma. Ma’auratan sun haifi ‘ya’ya uku tare kafin su rabu a shekarar 2022.