Babban limamin unguwar Mista Ali da ke karamar hukumar Bassa a jihar Filato, Imam Abdulkadir ya koka a kan satar ragon da aka yi masa.
Lamarin ya faru ne a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin a jajibirin Ed-el-Kabir.
Wani Limamin Al’ummar garin Malam Haruna Yaqub ne ya bayyana haka a lokacin wa’azin bayan Sallar Raka’a biyu, inda ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da bayyana shi a matsayin rashin hankali.
“Ragon Babban Limaminmu, wanda da gangan ya saya domin ya yanka, an sace shi da dare.
“A gaskiya mun kadu matuka da lamarin. Mun yi mamakin jin wannan labari.
“Wannan yana nufin mutane ba sa tsoron Allah. Abin ban tsoro ne a ce mutane sun kai ga satar ragon da ake nufi da ayyukan addini,” inji Yaqub.
Yakub ya kuma bukaci jama’a da su ji tsoron Allah su nisanta kansu daga sata ko duk wata muguwar dabi’a, yana mai jaddada cewa kowa zai amsa abin da ya aikata a duniya da lahira.
Ya ce: “Lokaci ya yi da mutane za su tuba kuma su ɗauki tafarkin Allah. Ba a makara ba. Ya kamata mutane su daina aikata munanan abubuwa kuma su yi aiki da dokokin Allah.