Iyalan wani dan sanda, Sufeta Kamarudeen Bello, da aka yi garkuwa da shi a wani masallaci a jihar Ogun a makon jiya, sun biya Naira 700,000 domin a sako shi a ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda Aminiya ta gano.
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki masallacin Soyoye da ke karamar hukumar Abeokuta ta Arewa a jihar, a makon jiya inda suka yi garkuwa da dan sandan da wasu masu ibada guda biyu.
Wata majiya ta ce, masu garkuwan sun tuntubi iyalan wadanda aka yi garkuwa, inda suka bukaci a biya duk wanda aka kashe Naira miliyan 5 kudin fansa.
Majiyar ta ce, “An tuntubi matar Insifeto Kamarudeen da lambar wayar daya daga cikin wadanda aka sace.”
Sai dai kuma an tattaro a ranar Lahadin da ta gabata cewa, dan sandan da sauran wadanda abin ya shafa sun samu ‘yanci bayan an biya kudin fansa.
“Ban san ko nawa ne kowannen su ya biya ba, amma ina ganin sufeton ‘yan sandan ya raba kusan Naira 700,000 kafin a sake shi,” inji wata majiya.
Hafsa, wanda kuma shi ne babban limamin masallacin, an bayyana cewa, matar Bello ta haifi jariri kwana hudu kafin faruwar lamarin.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da sace mutanen tare da sako mutanen a ranar Lahadi.
Oyeyemi, ya ce bai da masaniya ko an biya wani kudin fansa.