Yayin da ƙarin bayanai ke fitowa game da hatsarin jirgin sama da ya yi sanadiyar mutuwar Shugaban Iran Ebrahim Raisi, an gano cewa limamin da ke cikin jirgin tare da shi ya tsira daga hatsarin.
Imam Mohammad Ali Al-Hashem, shi ne limamin masallacin Juma’a na garin Tabriz, inda jirgin nasu ya nufa kafin hatsarin.
A cewar Mohammad Nami, shugaban hukumar kiyaye afkuwar bala’i ta Iran, ya tsira tsawon sa’a guda bayan faduwar jirgin. Har ma ya yi kokarin tuntubar taimakon ofishin shugaban kasar.
“Babu buƙatar gwajin DNA don gano fasinjojin da ke cikin jirgin,” in ji Nami.
Jimillar mutum tara ne suka mutu a hatsarin, waɗanda suka haɗa da ma’aikatan jirgin.