Likitoci a Indiya sun fara yajin aikin gama gari a ci gaba da nuna fushin da ake yi kan fyade da kisan da aka yi wa ɗaya daga cikin abokiyar aikinsu a wani asibitin Kolkata a makon jiya.
Kungiyar likitocin ƙasar ta ce, lokaci ne da ya kamata hukumomi su ɗauki matakai na tabbatar da tsaron lafiyarsu a asibitoci.
Ayyukan asibitoci da ba na gaggawa ba, za su kasance a rufe a faɗin ƙasar a ranar Asabar.
An shafe kwanaki mata na zanga-zanga tun bayan da aka tsinci gawar wata matashiyar likita a makon da ya gabata.
An kama mutum guda tare da tuhumarsa da aikata laifin, amma masu zanga-zangar sun ce matakin bai isa ba.