fidelitybank

Likitoci sun tsunduma yajin aiki na kwana 7 har sai an saki abokiyar aikin su wadda ta yi wata 8 a hannun ƴan bindiga

Date:

Ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasa (NARD), ta fara yajin aikin gargadi na kwana bakwai a dukkanin cibiyoyinta na faɗin ƙasa, inda ta buƙaci a sako Dakta Ganiyat Popoola, mambarsa da ke hannun masu garkuwa da mutane tsawon wata takwas.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito cewa shugaban NARD, Dakta Dele Abdullahi ne ya sanar da fara yajin aikin a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana cewa za a fara yajin aikin da ƙarfe 12:00 na safe a ranar Litinin 26 ga watan Agusta, 2024.

An yanke shawarar yajin aikin ne a wani taron gaggawa da jagororin ƙungiyar suka gudanar a ranar Lahadi, 25 ga Agusta, 2024.

An sace Dokta Ganiyat Popoola, magatakarda a sashin kula da ido da ke Babban Asitin Ido na ƙasa da ke Kaduna ne, kusan wata 8 da suka gabata, tare da mijinta da kuma ɗan uwanta.

Sai dai an saki mijinta a watan Maris, amma aka ci gaba da riƙe Popoola da dan uwanta.

Makonni da suka gabata, mambobin NARD sun yi zanga-zanga a dukkan manyan asibitocin ƙasar, don neman a gaggauta sakinta.

vgn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp