fidelitybank

Likitoci sun kai korafi Majalisa a kan hana su zuwa waje

Date:

Ƙungiyar kwararrun likitoci da likitocin haƙori da ke aiki a ƙasashen waje, ta shigar da ƙorafi ga Majalisar Dokokin Najeriya, kan ƙudurin da ke neman hana likitocin neman aiki a ƙasashen ƙetare har sai sun yi wa ƙasar hidima na wajibi na tsawon shekara biyar.

Cikin wata wasiƙa da aka yi wa take da : “Sanarwa kan matsayar ƙungiyar likitocin da ke aiki a kasashen waje – ƙudurin taƙaita wa sabbin kwararrun likitoci da na hakora barin Najeriya,” wadda aka rubuta a ranar 11 ga watan Afrilu 2023.

Jaridar The Punch a ranar Laraba ta ruwaito cewa an aika wa kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila wasiƙar.

Kazalika ta yi wa shugaban Majalisar Dattijai kwafi da shugaban kwamitin lafiya na Majalisa Dakta Ibrahim Oloriegbe; da kuma Dakta Tanko Sununu.

Kungiyar ta ce ƙudurin da Ganiyi Johson ya bijiro da shi wanda ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai a makon jiya, babu abin da zai kawo sai ci baya, kuma ba zai hana kwararrun ficewa daga Najeriya ba.

“Babban abin da ke janyo wannan matsala ita ce, rashin tsari mai kyau ga ɓangaren lafiya da ƙin zuba kuɗaɗe a ɓangaren na lafiya. Tsarin ƙasarmu ba ya taimaka wa kwararru, ko haɓɓaka kwarewarsu.

“Wasu ƙarin matsalolin su ne ƙarancin walwalar ma’aikata, rashin tsaro da rashin damar samun aiki ga sabbi har ma da tsofaffin waɗanda suka kammala karatu, ba a samun horaswa a kan lokaci, rashin biya yadda ya kamata.” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta ce tattaunawa ko kuma ɗaukar mataki kan wannan matsalar ba zai kawo ƙarshenta ba, dole sai an magance inda abin ya samo asali.

“Da yawan matasa na barin Najeriya ne domin samun rayuwa mai kyau, wannan matsala an daɗe ana fuskantarta sama da shekara 30 da suka gabata”.

latest legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp