Tawagar likitocin Yarima mai jiran gadon Saudiyya sun shawarce shi da kar ya yi doguwar tafiya a jirgi saboda kauce wa matsalar kunne da doguwar tafiya a jirgi ke haddasawa.
Hakan na zuwa ne bayan da mahaifinsa Sarki Salman ya umarce shi da ya jagoranci tawagar kasar zuwa taron kolin kasashen Larabawa da Aljeriya ke karbar baƙunci.
Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa likitocin masarautar ne suka fitar da sanarwar da kuma shawara ga Yariman ya dakatar da yin balaguron.
A don haka Sarki Salman ya umarci Ministan Harkokin Waje Yarima Faisal bin Farhan, ya wakilci kasar a madadin Yarima Muhammad.
Likitocin sun hana Yarima mai jiran gadon yin tafiya mai nisa a jirgi ne, “matukar ba za a tsaya wata kasa a huta ba, domin kaucewa matsalar kunne da doguwar tafiya a jirgi ke haddasawa, sakamakon tafiyar zuwa da dawowa ta kai tsawon awa 24.”
Sarki Salman ya ce, kasar Saudiya na tare da Aljeriya a kowanne hali, tare da nanata goyon baya ga duk matsayar da za a cimma a taron kolin.
Ranar 1-2 ga watan Nuwamba za a fara taron da za kasashe 31 na yankin gabas ta tsakiya za su halarta.


