fidelitybank

Likitoci sun dakatar da yajin aiki a jihar Nasarawa

Date:

Kungiyar likitocin ƙasa reshen jihar Nasarawa, ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar, inda ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin makonni biyu da ta biya musu dukkan bukatunsu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar ta tsunduma yajin aikin ne bayan gazawar gwamnatin jihar wajen aiwatar da ƙarin matsayi ga wasu mambobin kungiyar har na tsawon shekaru tara da ƙarin albashi sama da shekaru 12.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan taron gaggawa na majalisar da ta gudanar a Lafia babban birnin jihar, shugaban kungiyar a jihar, Dakta Peter Attah, ya bayyana cewa sun yanke shawarar dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar domin rage wahalhalun da al’ummar jihar suka shiga.

Attah ya ce kungiyar ta umarci mambobinta da su koma bakin aiki cikin gaggawa domin ceton rayuka.

Idan za a iya tunawa, tun a ranar 13 ga watan Yunin 2023 ne kungiyar ta ba da wa’adin kwanaki 21 don biya mata bukata kafin ta shiga yajin aikin na gargaɗi.

punch newspaper headlines today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp