Gwamnatin tarayya ta yi kira ga mambobin kungiyar likitoci ta kasa masu neman ƙwarewa NARD, da su janye yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai.
Karamin Ministan Lafiya Dr Tunji Alausa ne ya yi wannan kiran a ranar Alhamis a Kaduna yayin wata ziyara da ya kai cibiyar kula da ido ta kasa.
A cewar Alausa, ana ci gaba da tattaunawa don tabbatar da tsaron abokin aikinsu da aka sace, Dokta Ganiyat Popoola an sake ta.
“Muna kan maganar kuma mun tattauna da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu game da lamarin.
“Na yi magana da kwamishinan ‘yan sanda kuma kowa yana aiki tukuru don ganin an sake ta,” in ji shi.
Ministan ya ce ya gudanar da taro a ranar Litinin da ta gabata da shugabannin NARD kan lamarin domin shawo kan su janye yajin aikin domin hakan zai kara dagula lamarin.
Alausa ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun ci gaba da sauya bukatunsu a kowane lokaci amma jami’an tsaro suna bakin kokarinsu don ganin an ceto ta.
Idan dai za a iya tunawa ‘ya’yan kungiyar sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai domin ganin an ceto wani likita mazaunin Kaduna, Dokta Ganiyat Popoola.
An yi garkuwa da Popoola, ma’aikaciyar cibiyar ne a watan Disamba, 2023 kuma yanzu ya shafe kusan watanni tara a gidan masu garkuwa da mutane.
A halin da ake ciki, shugaban kungiyar na cibiyar kula da ido ta kasa Dr Ibrahim Mohammed ya ce har yanzu yajin aikin na ci gaba da yaduwa.
Ya ce masu ba da shawara kan harkokin kiwon lafiya da na hakori ne suka shiga yajin aikin kuma umarni ne daga hukumar ta kasa.