Tsohon dan majalisar dokokin Najeriya, Shehu Sani, ya yi kira ga kungiyar likitocin ta kasa, NMA, da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa, NANNM, da su gayyato dukkan masu neman takarar shugaban kasa domin a gwada lafiyarsu.
Sanata Sani ya ce hakan zai taimaka wajen daidaita cece-kucen da ake fama da shi kan yanayin lafiyar wasu ‘yan takara a zabe mai zuwa.
Bayanin hakan na kunshe ne a wani sako da ya fitar ta shafin sa na Twitter da aka tabbatar a ranar Alhamis.
Ya kuma ba da shawarar cewa idan an gudanar da shi a bayyana sakamakon.
Ya rubuta cewa, “Kungiyar Likitoci ta Najeriya NMA da kungiyar ma’aikatan jinya NNNM, yakamata su gayyaci duk masu neman takarar shugaban kasa don yin cikakken gwajin lafiya, kuma su bayyana sakamakon a bainar jama’a. Wannan zai warware cece-kuce kan yanayin lafiyar masu takara.”