Mai yin rijistar ƙungiyar likitocin haƙori da sauran likitoci masu neman kwarewa Dr Fatima Kyari, ta bayyana cewa likitocin da suka yi rijista ba su wuce 58,000 da suka sake sabunta lasisinsu na aiki a 2023 saboda zirarewar kwararrun lafiya zuwa ƙasashen waje.
Dr Kyari ta bayyana hakan ne yayin rantsar da sabbin likitocin 20 da aka yi bikinsu a Jami’ar jihar Edo.
Tana cewa wajibi ne ga dukkan wanda aka rantsar ya yi aiki da ƙa’idoji da kuma tsari na yadda likitoci ke aiki a Najeriya.
Tace hukumar su na da mutum 130,000 da suka yi rijista ya zuwa yanzu a matsayin likitoci da ke son aiki a Najeriya tun lokacin da ta fara aiki shekara 61 baya.
“Amma 58,000 ne kacal suka sabunta lasisinsu na shekara-shekara a 2023, wannan na da alaƙa da yadda ake samun ƙaruwar likitocin da suke zirarewa ƙasashen ƙetare.”