Ƙungiyar likitoci ta Legas (Medical Guild), wacce ke ƙarƙashin gwamnatin jihar, ta fara yajin aikin gargaɗi na kwana uku saboda rage musu albashi ba tare da sanarwa ba.
A wata sanarwa da shugabannin ƙungiyar, Dr Japhet Olugbogi da Dr Adekunle Akinade, suka fitar, sun ce gwamnatin jihar ta rage albashin likitoci a watan Yuli ba tare da wata shawara ko sanarwa ba, duk da halin matsin tattalin arziki da ake ciki.
Ƙungiyar ta ce sun tattauna da gwamnati bayan hakan, kuma an kafa kwamiti don sasanta lamarin, amma duk da haka, an sake rage albashin a watan Yuli, wanda suka bayyana a matsayin rashin adalci da saɓawa doka.
Likitocin sun ce “mafi girman albashin babban likita a Legas bai kai dala 1,100 ba, amma gwamnati ta zaɓi rage wannan kuɗin maimakon ƙarfafa gwiwarsu.”