Wasu rahotanni daga kasar Libiya na cewa, wani bangare na hukumomin kasar, sun kama wasu ƴan kasashen Afrirka bakin haure bakaken fata yawanci ƴan asalin kasar Jumhuriyar Nijar da Najeriya sama da 900.
Sama da wata daya da ake rike da wadannan mutane sai dai har zuwa yanzu babu wani cikaken bayani game da inda suke.
Tuni wasu da suka galabaita daga ciki suka fara mutuwa.
Wani daga wadanda suka tsira a lokacin da aka kai samamen da jami’an tsaro suka kai a lokacin da suka kama ƴan Afirkar ya shaida wa BBC cewe ” Ranar 6 ga watan Satumba ne jami’an tsaron suka kai samame, suka kama mutanen Nijar da Najeriya, ” Nima ina cikin mutanen amman na gudu ne shiyasa ba a kama ni ba, amman sun dauki mutanen da suka kai 500 a lokacin.”
“Daga baya cikin wadanda suka kama din basu anshe amsu wayoyi ba, sune suka kira suke fadin cewa adadin mutanen da aka kama sun kai 900 kuma yawancinsu ƴan Nijar ne” cewar mutumin.
Wasu daga cikin farar hula na Nijar din na ci gaba da kira ga hukumomin ƙasar da su sanya baki kan lamarin. In ji BBC.