Babban jami’in agajin gaggawa na Majalisar Ɗinkin Duniya, Martin Griffiths, ya ce matsalolin da ake fuskanta a Libya sanadin ambaliyar ruwa su ne: matsuguni da abinci da kuma buƙatun kula da lafiya.
Mista Griffiths ya ce ba a san girman bala’in da ya faru ba, saboda rarrabuwar kawuna tsakanin masu mulkin ƙasar, kuma a cewarsa ya zama wajibi a samu hadin kai tsakanin ɓangarorin biyu.
Da yake jawabi yayin wani taro a birnin Geneva, babban jami’in ya zayyano manyan ƙalubalan da ya ce hukumomin bayar da agaji na fuskanta a Libya.
Ya ce “Ina jin, matsalar da muke da ita a Libiya, ita ce samar da haɗin kai tsakanin gwamnatoci guda biyu a Libiya.
Na biyu shi ne tabbatar da gano haƙiƙanin tushen matsalar da ake ciki. A yanzu ba ma cikin Libiya, saboda haka ba za mu iya sanin girman matsalar ba, ambaliyar ruwan da asarar da aka tafka waɗanda suka shafi dukiya da gidajen jama’a da suka rushe.”
“Hakan ya sa hankali ya karkata ta yadda ba za a iya tantance ainihin bukatar da ake da ita da kuma gane adadin waɗanda suka mutu ba,” in ji shi.
“Ga kuma bukatar tabbatar da kayan agaji sun isa ga mabukata, kuma akan lokaci. Wannan ne ma ya sa haɗin kai ke da muhimmanci.”
“Babu wanda zai iya sanar da kai iya yawan ta’adin da iftila’in ya haifar saboda farraƙar da ake da ita a Libya.
Hamid Al-Mabrouk Abdel-Rahman, ƙwararren likitan masu fama da taɓin ƙwaƙwalwa ne, ya ce ayarin abokan aikinsa za su ziyarci biranen da ke kusa da gaɓar teku.
“Mun durfafi biranen Benghazi da Derna da kuma Al-Bayda, waɗanda lamarin ya shafa domin bayar da agaji ga mutanen da suka samu kansu a wannan bala’i.”
A cikin jami’an, akwai likitocin ƙashi da likitocin fiɗa da ma’aikatan jinya da ƙwararru a ɓangare tsafta, sun shirya domin yin aiki kafa-da-kafada
Ƙungiyar ba da agaji ta Red Crescent a Libya, ta ce bayan aukuwar ambaliyar ruwan, har yanzu ba a cire fatan samun ƙarin wasu da rai ba, duk da yake, tuni aka bayyana mutuwar akalla mutum 11,000, baya ga ɓatan ƙarin wasu dubban.


