Bayer Leverkusen ta kafa sabon tarihi a kwallon kafar Jamus bayan ta buga wasa 33 ba tare da an ci ta ba, bayan nasarar da ta yi a gasar Bundesliga kan Mainz.
Ƙungiyar ta Xabi Alonso yanzu ta bai wa Bayern Munich da ke biye mata a matsayi na biyu tazarar maki 11 a saman teburi.
Granit Xhaka ne ya fara ci wa Leverkusen kwallo a minti uku, kafin Dominik ya farke ta ta zama É—aya da É—aya.
Robert Andrich ne ya jefa kwallo ta biyu bayan wani dogon hari da yakai daga nesa ami tsaron ragar Mainz ya ci kansu.