Likuena ta Lesotho za ta isa Uyo a ranar Litinin yau dinnan domin karawa da Super Eagles ta Najeriya wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2026 a karo na daya.
Bangaren Leslie Notsi za su yi balaguron ne daga birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
Ana sa ran ‘yan wasan da jami’ansu za su tashi kai tsaye zuwa filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas kafin su kara wani jirgin zuwa Uyo.
Kungiyar Likuena ta fara shirye-shiryen tunkarar wasan a birnin Johannesburg ranar Juma’ar da ta gabata.
A ranar Alhamis ne Lesotho za ta kara da Super Eagles a filin wasa na Godswill Akpabio International Stadium dake Uyo a jihar Akwai Bom.
Za su karbi bakuncin Squirrels na Jamhuriyar Benin a wasansu na gaba a filin wasa na Moses Mahbida a ranar Talata 21 ga watan Nuwamba.