Legas ta kasance jihar da ta fi kowacce yawan masu amfani da bayanan intanet a Najeriya.
Jihohin Ogun da Kano yayin da jihohin uku ke da kashi 23.8 cikin 100 na yawan masu amfani da intanet a kasar.
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana hakan a ranar Talata a cikin bayananta na sadarwa: Active Voice and Internet, Porting and Tariff Information Report na farkon kwata na 2022, wanda aka buga a gidan yanar gizon ta.
A cewar NBS, masu amfani da Intanet a Najeriya sun karu kadan da kashi 0.62% duk shekara zuwa miliyan 145.85 a watan Maris na 2022 idan aka kwatanta da masu amfani da Intanet miliyan 144.95 da aka samu a daidai lokacin shekarar 2021.