fidelitybank

Legas ce ta 19 mafi dadin zama a duniya

Date:

Kamfanin ‘Time Out’ da ke lura da ƙididdigar daɗin zama a biranen duniya ya ce birnin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ne birni na 19 mafi daɗin ziyarta a duniya.

Kamfanin ya wallafa jadawalin birane 50 da ya ce sun fi daɗin zama daga cikin fiye da birane 20,000 da ya gudanar da bincike a kansu a faɗin duniya.

Birnin New York na Amurka ya kasance birni na farko mafi daɗin ziyarta a duniya, daga nan sai birnin Cape Town na Afirka da Kudu a matsayi na biyu da birnin Berlin na Jamus a matsayi cikin birane 50 na duniya.

Kamfanin ya yi amfani da wasu ƙa’idoji wajen fitar da jawadalin inda suka haɗar da ingancin abinci da kuma sauƙinsa da al’adu da rayuwar cikin dare da ake yi a birni.

Sauran ka’idojin su ne yadda mazauna birnin ke ji da shi da irin manyan mutanen da ke rayuwa a birni, da wuraren shaƙatawa da na tarihi da sauran abubuwa.

Kamfanin ya ce Legas birni ne da kowa zai iya ziyarta ”da wanda ya saba rayuwa a tsibiri da wanda ya saba rayuwa a kan tudu, kowa zai ji daɗin birnin Legas, wanda shi ne birnin da ya fi kowanne mutane a nahiyar Afirka”.

Biranen London da Madrid sun kasance a matsayi na huɗu da na biyar, sai biranen Mexico City da Liverpool da kuma Tokyo da Rome da kuma Porto ke biye musu.

news nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp