Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta ce ta kama mutane 3,359 masu safarar muggan kwayoyi, inda aka daure kasa da mutane 677 a gidan yari tare da kama wasu kwayoyi tsakanin watan Janairu zuwa Maris 2022.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar, hukumar ta ce, akalla mutane 2,223 masu shaye-shayen kwayoyi ne kuma aka basu shawarwari ta hanyar takaitaccen aiki tare da gyara su a cibiyoyin NDLEA dake fadin kasar nan a cikin wannan lokaci.
Rahoton ya kara da cewa Legas ce ta fi kowacce jiha yawan masu safarar miyagun kwayoyi inda aka samu kilogiram 22,192.62 na haramtattun abubuwa daga sassan jihar, sai kuma hukumar filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport (MMIA) da ke Ikeja, shi ma a Legas, an kama kwayoyi masu nauyin kilogiram 8,979.869. .
Kano da Kaduna ne suka jagoranci tawagar wajen kama masu laifin tare da kama mutane 194 a kowace jiha a cikin lokaci guda.
Hukumar ta ce an lalata gonakin tabar wiwi sama da hekta 257 a dazuzzukan jihar Ondo.